Shugaban hukumar Ilimin bai daya ta Jihar jigawa ya nemi hadin kan hukumomin makarantu da limamai

0 177

Aisha Muhammad lawan

Shugaban hukumar Ilimin bai daya ta Jihar jigawa Farfesa Haruna Musa yayi kira ga hukumomin makarantu da limamai su baiwa hukumar hadin kai a kokarin da take wajen ganin an koma makaranta a kan lokaci ba tare da an samu wata tangarda ba,domin samun sakamako mai kyau a fannin koyo da koyarwa a fadin Jihar.

Shugaban hukumar yayi wannan kira ne yayin ganawa da shugabannin kungiyar Iyayen yara da,da kuma limaman masallatai na masarautun Jigawa, yayinda ake shirye-shiryen komawa makaranta a zangon karatu na shekarar 2023/2024.

Farfesa Haruna Musa, ya bukaci limaman masallatan Juma’a da suyi amfani da hudubobin juma’a wajen jan hankalin Iyayan yara da malaman makaranta dangane da nauyin da ya rataya a kan su na samar da cigaba a fannin ilimi dama halartar makaranta a kowanne lokaci.

Yayin ganawar, an tattaunawa batutuwa da dama dangane da shiryen-shiryen komawa a makaranta a zangon karatu na farko.

A nasu jawabin,masu baiwa gwamna shawara da sanya ido kan harkokin ilimi,Limamai, shugabannin kungiyar Iyayen yara da kuma shugabannin hukumomin ilimi karkashin hukumar ilimin bai daya ta Jiha, sun yabawa shugaban hukumar dangane da irin kokarin da yake wajen habaka fannin ilimi tare dayin alkawarin basu goyan baya domin cigaban matasa masu tasowa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: