Hukumar NCDC ta ce ƙarin mutum 48 sun kamu da cutar korona

0 111

Hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce ƙarin mutum 48 sun kamu da cutar korona ranar Alhamis.

Rahoton da hukumar ta wallafa ya ce a jiha tara aka samu sabbin waɗanda suka kamun, ciki har da Abuja babban birnin ƙasar.

Jihohin su ne Legas-15, Cross River-12, Abuja-8, Plateau-7, Ogun-2, Abia-1, Delta-1, Oyo-1, Rivers-1

Zuwa yanzu, jumillar mutum 253,923 ne suka kamu da cutar a Najeriya, sannan ta yi ajalin mutum 3,139.

Leave a Reply

%d bloggers like this: