Hukumar NDLEA Ta Damke Ƙatuwar Mota Maƙare Da Wiwi A Kano

0 219

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a jihar Kano ta samu nasarar kama wata mota da ke ɗauke da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 103, wacce ta taso daga Zariya zuwa Kano Babban kwamandan rundunar a jihar Kano Ibrahim Abdul ne ya bayyana wa manema labarai a lokacin da rundunar ta yi holin wasu dillalan miyagun ƙwayoyi a hedkwatar rundunar da ke Kano.

Ibrahim Abdul ya ce matuƙin motar ya fara rarrabawa dillalan tabar wiwin tabar ne tun daga Zariya, kafin ya iso Kano.Ya ƙara da cewa rundunar ta yi nasarar damƙe dillalan ƙwaya fiye da mutum 50 a Kano, kuma an same su da miyagun Ƙwayoyi masu nauyin kilogiram 720, wanda kuma za’a gurfanar da su a gaban kuliya.

A ƙarshe babban kwamandan ya buƙaci gwamnatin jihar Kano da ta taimaka wajen kammala ginin cibiyar lura da masu ta’amali da miyagun ƙwayoyi da aka fara ginawa a hedikwatar rundunar da ke Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: