

- Gwamna Zulum ya raba wa likitoci fiye da 80 didaje da kudi Naira miliyan 79 don inganta rayuwarsu - July 2, 2022
- Manyan Sarakunan kasar Yarabawa sunyi kiran samun zaman lafiya daga gwamnati kafin zaben 2023 - July 2, 2022
- Kasar Jamus za ta fara dawo wa da Najeriya dubban kayayyakin tarihin ta da aka wawushe tun lokacin mulkin mallaka - July 2, 2022
hukumar tara kudaden shiga ta jihar Borno ta tuhumi hukumomi 7 na majalisar dinkin duniya da laifin kin biyan haraji.
Hukumomin 7 a cewar hukumar sun hada da ofishin kula da agaji na majalisar dinkin duniya da ofishin kula da ‘yan gudun hijira na majalisar dinkin duniya da asusun yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) da shirin abinci na majalisar dinkin duniya da shirin cigaba na majalisar dinkin duniya da shirin abinci da noma da kuma hukumar lafiya ta duniya (WHO).
Hukumar tara kudaden shigar tace duk da kasancewar dokokin kasa da kasa dake kula da ayyukan majalisar dinkin duniya sun ciresu daga biyan haraji, hakan bai shafi ma’aikatansu ba, musamman wadanda ke zaune a jihar da kuma masu kwantiragi.
Shugaban hukumar tara kudaden shiga ta jihar Borno, Mohammed Alkali, ya sanar da haka yayin taron manema labarai a Maiduguri, babbban birnin jihar.
Mohammed Alkali yayi nuni da cewa gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, na sane da halin da ake ciki.