Hukumar Yaki da Cuta mai karya garkuwar jiki ta Kasa (NACA) ta horas da mata 80 sana’o’i daban-daban a Jihar Jigawa

0 97

Hukumar Yaki da Cuta mai karya garkuwar jiki ta Kasa (NACA) ta horas da mata 80 sana’o’i daban-daban a Jihar Jigawa.

Daraktan ayyuka na musamman na hukumar, Baidi Gajo Elleman ne ya bayyana hakan a wata zantawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa a jiya.

Gajo Elleman ya ce an zabo wadanda suka ci gajiyar shirin ne daga kananan hukumomin Birniwa, Guri da Kirikasamma.

Ya bayyana cewa an horas da matan ne kan gyaran gashi da gyaran fuska da kwalliya, inda ya kara da cewa an yi hakan ne don baiwa wadanda suka amfana damar dogaro da kai da kuma samar da sana’o’i.

A cewarsa, an baiwa kowace daya daga cikin matan naira dubu 75 a matsayin jarin fara kasuwanci.

A saboda haka ya bukaci wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da kudaden wajen inganta rayuwarsu da tattalin arzikin iyalansu da al’ummarsu da jiha da ma kasa baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: