‘Sai an mallaki katin shedar allurar korona kafin dalibai su rubuta jarabawar JAMB’

0 87

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB, ta yi karin haske kan cewa dalibai ‘yan kasa da shekara 18 ba a bukatar su gabatar da katin rigakafin corona kafin a ba su damar shiga dakunan jarrabawar JAMB.

Wata sanarwa da ta fitar a jiya mai dauke da sa hannun shugaban sashin yada labaran hukumar ta JAMB, Fabian Benjamin, ta ce wadanda aka nemi su gabatar da katin rigakafin sune wadanda dokar NCDC ta rigakafi ta shafa.

Hukumar jarrabawar dai ta ce za ta bukaci shaidar shekaru domin baiwa duk wani mai karancin shekaru damar shiga wuraren jarabawar.

Hukumar shirya jarabawar a cikin sanarwar da ta fitar ranar Litinin, ta bayyana cewa ba za a bari wani mutum ya shiga wajen rubuta JAMB a duk fadin kasarnan ba, sai ya nuna katin rigakafin corona.

Kafin JAMB, hukumar matasa masu yiwa kasa hidima (NYSC) ta sanar da cewa wadanda aka yiwa rigakafin corona ne kadai za a baiwa damar yiwa kasa hidima a shekara mai zuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: