Jami’ar Tarayya dake Dutse za ta binciki yawaitar samun ciwon koda a yankin kogin Hadejia

0 80

Jami’ar Tarayya dake Dutse tace za ta binciki yawaitar samun ciwon koda a yankin kogin Hadejia, bisa tallafin asusun bincike na kasa.

Jagoran masu binciken, Dr. Muhammad Isa Auyo, shugaban sashen kimiyyar rayuwa na jami’ar, shine ya sanar da haka cikin wata sanarwa da aka aiko mana nan gidan rediyon Sawaba.

Yace asusun tallafawa manyan makarantu na TETFund ya saki kudi naira miliyan 36 domin gudanar da binciken.

Za a gudanar da binciken da nufin gano wasu sinadarai wadanda ke haifar da ciwon koda ga mutanen dake rayuwa a yankin kogin Hadejia.

Binciken zai kuma yi kokarin gano wasu sinadarai masu illa da ake samu a kogin Hadejia cikin shekara 30 da suka gabata, sanadiyyar amfani da maganin kwari da na kashe ciyawa.

Sinadaran, a cewarsa, zasu iya shafar kayayykin abinci musamman kayan marmari, da ruwa da kifi, wadanda mutane ke ci, kuma hakan zai iya zama silar yawaitar samun ciwon koda a yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: