Mutum biyar sun samu raunuka daban-daban a wani rikici tsakanin manoma da makiyaya a Malam Madori a jihar Jigawa

0 95

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta ce akalla mutane biyu ne suka mutu a wani rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar.

Kakakin rundunar ‘yansandan jiharnan, ASP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

Ya ce lamarin ya faru ne a karamar hukumar Taura.

A wani batun kuma, Shisu Adam ya kuma bayyana cewa irin wannan lamari ya faru a Gandun Galadima da ke karamar hukumar Malam Madori.

Ya ce a sakamakon faruwar lamarin mutane biyar sun samu raunuka daban-daban kuma an garzaya da su babban asibitin Hadejia domin kula da lafiyarsu.

Ya kara da cewa an tabbatar da mutuwar wani matashi mai suna Yakubu Saleh na Gandun Sarki, dan shekaru 30 a duniya a lokacin da yake jinya a asibiti.

Kakakin ya ce an kama mutane biyar da ake zargi da hannu a lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: