Hukumar INEC ta mayar da martani ga jam’iyyar PDP kan batun taron NEC da suke shirin gudanarwa, inda ta bayyana cewa sanarwar taron ba ta cika ka’idar da ake bukata ba, bisa doka da tsarin jam’iyyun siyasa.
A wata wasika da Haliru Aminu, sakataren hukumar na riko ya sanyawa hannu, an ce sai shugaban jam’iyya da sakataren jam’iyyar na ƙasa ne za su haɗa hannu wajen tura irin wannan sanarwa zuwa INEC.
A gefe guda kuma, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da ginin sabuwar hedkwatar INEC a Abuja, yana mai cewa wannan gini alama ce ta ƙarfafa dimokuraɗiyya da ’yancin hukumar.
Ministan Abuja, Nyesom Wike, wanda ke jagorantar aikin, ya ce an amince da aikin ne tun watan Maris din 2025, kuma za a kammala shi kafin ƙarshen wa’adin shugaba Tinubu.