Gwamnati jihar jigawa ta ware naira biliyan biyu domin gina magudanan ruwa da gadaje guda arba’in da daya don dakile ambaliya a fadin jihar.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr. Nura Ibrahim ne ya bayyana haka yayin bikin ranar yaki da fari da hamada ta duniya da aka gudanar a cibiyar horar da ma’aikata da ke Dutse tare da hadin gwiwar ACRESAL.
A jawabin da sakataren dindindin na ma’aikatar, Dr. Abdullahi Namadi ya karanto, an bayyana cewa aikin zai fi mayar da hankali ne a yankunan da ke fuskantar barazanar ambaliya da kuma yaduwar hamada da tabarbarewar muhalli. Gwamnatin ta kuma fara kokarin farfado da kasar noma da aka lalata tare da sayen manyan injina guda biyu domin yashe Kogin Hadejia, da kuma dakile yankan rijiya mai zurfi a jihar, yayin da hukumar JISEPA ke aiki da kungiyoyi daban-daban wajen horar da matasa da mata kan tattara shara domin amfani da ita.