Rahoton Hukumar Kididdiga ta Kasa ya bayyana cewa Najeriya ta shigo da danyen man fetur na sama da naira tiriliyan 1.19 a cikin watanni uku na farkon wannan shekarar, saboda karancin isasshen man gida da zai wadatar da matatun cikin gidan.
Rahoton ya nuna cewa kasar Amurka ce ke kan gaba wajen samar da wannan danyen mai da aka shigo da shi, wanda ya kai kusan kashi 61 cikin 100 na jimillar shigowar danyen mai, sai kasar Angola da Aljeriya.
Wannan yanayi ya sake jaddada matsalar da ke damun masana’antar mai a Najeriya, inda matatun cikin gida ke komawa kasashen waje domin samun man da za su tace.
Kungiyar masu matatun mai a Najeriya ta koka da cewa har yanzu ba su samu kaso ko kadan daga tsarin rabon danyen mai na cikin gida (DCSO) da dokar masana’antar man fetur ta 2021 ta tanada ba, inda ake zargin masu hakar mai da sayar da shi a waje saboda ribar canjin kasashen waje.