Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura sunayen mutum 17 da ya ke so su jagoranci manyan kwamishinonin jihar Rivers, kuma yanzu haka an fara tantance su a gaban kwamitin wucin gadi na Majalisar Dattawa.
Wadanda aka zabo sun hada da wadanda za su rike hukumar zabe ta jihar, hukumar ma’aikata da kuma hukumar kula da ma’aikatan kananan hukumomi, kuma dukkansu sun riga sun cika sharuddan hukumar ladatar da ma’aikatan gwamnati ta kasa, ciki har da bayyana kadarorinsu.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya tabbatar da cewa dukkan wadanda aka mika sunayensu ba su da matsala ta tsaro, domin an tantance su daga hukumar DSS da rundunar ‘yan sanda. An kuma tabbatar da cewa babu wani koke da aka shigar a kansu, kuma bayan kammala tantancewar, za a mika rahoto ga zauren Majalisa domin amincewa ko kin amincewa da nadin nasu.