Gwamnatin Benue ta sanar da hutu a yau Laraba 18 ga Yuni domin maraba da ziyarar shugaba Tinubu

0 653

Ana cigaba da shirin karɓar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Jihar Benue, inda gwamnati ta sanar da hutun a yau Laraba, 18 ga Yuni, domin maraba da ziyarar shugaban.

A yammacin ranar Litinin, 17 ga Yuni, ma’aikata sun fara gyaran manyan hanyoyi da sare ciyoyi a birnin Makurdi, musamman a kan hanyar da zai bi daga filin jirgin sama zuwa gidan gwamnati.

Wannan na zuwa ne bayan rahotanni da ke cewa fiye da mutane 200 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan harin da ake zargin makiyaya ne suka kai a daren ranakun 13 zuwa 14 ga Yuni.

A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, an nuna yadda jami’ai da ma’aikata ke tsabtace guraren, yayin da kungiyoyin goyon baya ke shirya wani gangamin maraba na musamman da aka bayyana da suna “gaf da kafa”.

Leave a Reply