Shugaba Bola Tinubu zai gana da manyan shugabanin jihar Benue a Yau Laraba

0 141

Shugaba Bola Tinubu zai gana da manyan masu ruwa da tsaki a jihar yau Laraba domin jin korafinsu kai tsaye, da nufin kawo karshen rikicin dake asarar rayuka da dukiyoyin al-umma a jihar Benue.

Ganawar na zuwa ne kwanaki bayan fiye da mutum 200 sun rasa rayukansu a garin Yelewata, karamar hukumar Guma, bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki da makamai masu linzami tare da kone gidaje.

Majalisar dokokin jihar ta bayyana cewa Gwamna Hyacinth Alia da mataimakinsa Sam Ode da ‘yan majalisar sun kasa cika alkawarin kare rayuka da dukiyoyin al’umma. A yayin da jam’iyyun adawa da kungiyoyin farar hula ke kiran a ayyana dokar ta baci, Shugaban kasa ya ce lokaci ya yi da za a wanzar da zaman lafiya da fahimtar juna, tare da baiyana cewa za a aiwatar da tsauraran matakan tsaro bayan ziyarar Hafsan Sojoji da Sufeto Janar na ‘Yan sanda zuwa wurin da aka kai harin.

Leave a Reply