Isra’ila ta ce sojojinta sun kaddamar da hari na tsakar dare kan Hamas a tsakiyar Gaza

0 317

Isra’ila ta ce sojojinta sun kaddamar da hari na tsakar dare kan Hamas a tsakiyar Gaza, inda suke nausawa yankunan da ke wajen sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat wanda ayyukan sojin bai lalata sosai a baya ba.

Sojojin sun yi ruwan hare-hare ta sama kafin daga bisani wasu suka danna yankin ta kasa, kuma mutum biyar ne suka mutu a harin.

A ɓangare guda kuma, an kashe wani Bafalasɗine,da jikkata wasu 25 bayan yahudawa ‘yan kama wuri zauna sun afkawa kauyen al-Mughayyir da ke kusa da birnin Ramallah a Gaɓar Yamma.

Lamarin ya faru bayan sojin Isra’ila da dakaru na musamman sun zo neman wani yaro ɗan shekara 14 da ya ɓata. Benjamin Achimeir ya fito kiwon dabbobi daga wani matsugunin ‘yan kama wuri zauna da ke kusa da kauyen, tun daga lokacin ba a kara ganinsa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: