Kungiyar kwadagon ta kasa ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta bayyana sabon mafi karancin albashi

0 239

Kungiyar kwadagon ta kasa ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta bayyana sabon mafi karancin albashi a ranar 1 ga watan Mayu. Mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta kasa, Tommy Etim, wanda ya zanta da wakilinmu, ya bayyana ranar ma’aikata a matsayin wata Babbar rana ga ma’aikatan. Ya yi nuni da cewa akwai tsammani da yawa musamman ganin yadda wasu sabbin tsare-tsare na gwamnati suka ci gaba da jefa ‘yan Najeriya cikin talauci. Etim ya ce ma’aikata a kasar na sa ran samun sabon mafi karancin albashi mai tsoka. Menema labarai sun ruwaito cewa kungiyoyin kwadago da suka hada da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC, sun bukaci Naira Dubu dari 6 da 15, a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikata a kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: