Jagoran darikar Tijjaniyya a Najeriya ya bayyana goyon bayansa ga gwamnatin Bola Tinubu

0 137

Mai martaba Sarkin Kano na 14 kuma jagoran darikar Tijjaniyya a Najeriya ya bayyana goyon bayansa ga gwamnatin shugaban Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa shugaban ya karbi mulki a cikin mawuyacin hali.

Don haka ya yi kira ga masu rike da mukaman siyasa da su kawo karshen adawa su maida hankali wajen gudanar da mulki.

Tsohon gwamnan na kudi ya yi wannan jawabi ne a Legas a karshen mako a wajen bikin Maulidin fiyeyyen halitta da Jam’iyyatu Ansariddeen Attijaniyya ta shirya.

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shetima wanda shima ya halarci taron ya ce shugaba Tinubu ya fahimci nauyin amanar da al’ummar Nijeriya suka dora masa, ya kuma yi alkawarin cewa zai yi shugabanci cikin tausayi da adalci da dai-daito.

Ya kuma yi alkawarin cewa za a kare hakkin dukkan ‘yan Nijeriya, ba tare da la’akari da addini ko kabila ba, a karkashin wannan gwamnati. Inda ya bukaci mutane da su yi koyi da kyawawan dabi’un manzon Allah cikin mu’amalarsu ta yau da kullum.

Leave a Reply

%d bloggers like this: