An kama wani da ake zargi da satar janareton masallacin Juma’a

0 115

Jami’an ‘yan sanda a jihar Kaduna sun kama wani da ake zargi da satar janareto mai amfani da hasken rana da batirinsa da ke samar da haske a masallacin Juma’a a garin Hunkuyi da ke karamar hukumar Kudan ta jihar.

Da yake tabbatar da kamun, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya ce jami’an ‘yan sandan yankin sun cafke wani Basiru Rabi’u na Sabon Gari mai suna Hunkuyi da laifin aikata laifin.

Ya bayyana cewa, an kama wanda ake zargin ne a lokacin da mutanen yankin suka yi shakku kan motsin da suke ji a masallacin.

Daga baya an kama wanda ake zargin kuma bayan bincike ya amsa laifin satar na’urar mai amfani da hasken rana da batirin sa. Sai dai kakakin yansandan ya ce an kama wanda yake sayarwa irin wannan kaya idan ya sato, yayin da yake cigaba da amsa tambayoyi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: