Gwamnatin jihar Jigawa ta ware kudi Naira biliyan daya domin aiwatar da tsarin inshorar lafiya

0 177

Gwamnatin jihar Jigawa ta ware kudi naira biliyan daya a wannan shekarar domin aiwatar da tsarin biyan inshorar lafiya na jama’a a karkashin hukumar inshorar lafiya ta jihar Jigawa.

An yi shirin ne don samar da garanbawul na kiwon lafiya kyauta ga ƴan ƙasa marasa galihu 500 a kowace mazaba a faɗin jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Muhammad Abdullahi Kainuwa shi ne ya sanar da haka a lokacin da yake karbar kayan aikin kiwon lafiya na miliyoyin naira wanda wata gidauniyar kiwon lafiya ta Amurka a Najeriya mai suna George Town Global Health Nigeria ta samar.

Ya yabawa gidauniyar bisa wannan karamci inda da ya ce zai karawa shirin gwamnatin Jigawa na inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a fadin jihar.

Kwamashinan lafiyar ya kuma tabbatar da cewa, zasu yi amfani da kayyayakin yadda ya kamata. Tun da farko yayin da yake gabatar da kayayyakin tallafin, shugaban kungiyar na kasa Bashir Zubairu, yace kayayyakin za’a yi amfani dasu wajen bunkasa harkokin kiwon lafiyar jama’ar jihar Jigawa, musamman wajen cututtukan mata masu juna biyu da kananan yara, da kuma cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV.

Leave a Reply

%d bloggers like this: