Jami’ar FUD Ta Kere Sa’a – A.A Rasheed

0 88

An bayyana Jami’ar gwamnatin tarayya dake Dutse babban birnin jihar Jigawa, a matsayin jami’ar da ta fi fice a cikin jami’oi 12 da gwamnatin tarayya ta gina a 2011.

Shugaban hukumar dake kula da jamioi ta kasa (NUC) Farfesa Abubakar Adamu Rasheed ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja.

Ya ce jami’ar ta FUD ta kaddamar da bikin sababbin dalibai har sau 8 daga cikin wadanda aka kirkire su tare yayin da su kuma ke kokarin gudanarda bikin a karon farko.

Farfesa Abubakar Adamu Rasheed ( Shugaban hukumar dake kula da jamioi ta kasa (NUC) )

Rasheed ya ce an samu cigaba sosai a jami’ar sakamakon fadi tashin da shugabannin jami’ar ke yi karkashin jagorancin Farfesa JD Amin, da kuma Farfesa Fatima Batul-Muktar.

Kazalika ya yabawa al’ummar jihar Jigawa da kuma gwamnatin jihar  bisa taimakon jami’ar wajen gudanar da ayyukanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: