Jam’iyyun PDP, ADC da LP sun soki jam’iyyar APC bayan Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya sauya sheka daga NNPP zuwa jam’iyyar mai mulki, suna cewa hakan ba zai shafi sakamakon zaben 2027 ba.
Shugabannin yada labaran PDP da ADC sun bayyana cewa sauya shekar gwamnan alama ce ta gazawar ɗabi’a ba ƙarfin siyasa ba, inda suka jaddada cewa hakan bazai jawo kuri’un jama’a ba.
Shugabar rikon kwarya ta LP, Sanata Nenadi Usman, ta gargadi jama’a da kada su ruɗu da sauya shekar manyan ‘yan siyasa.
A nasa bangaren, daraktan yada labarai na APC, Bala Ibrahim, ya tarbi Gwamna Yusuf, yana mai cewa dawowarsa ta ƙara ƙarfafa jam’iyyar da tabbatar da manufofinta na dimokuraɗiyya.
Gwamna Yusuf ya sanar da ficewarsa daga NNPP duk da goyon bayan Rabiu Musa Kwankwaso, lamarin da ya zo bayan makwanni na raɗe-raɗin siyasa da tashin hankali a Kano.
Jam’iyyar NNPP ta bayyana matakin a matsayin cin amanar al’ummar Kano, tana mai cewa tarihi ya nuna masu sauya sheka ba sa tsira daga hukuncin jama’a.
Duk da adawar jam’iyyun, ana sa ran Gwamna Abba Yusuf zai kammala shiga APC a yau tare da manyan ‘yan majalisar jihar da shugabannin kananan hukumomi, lamarin da ke nuna gagarumin sauyi a siyasar Kano.