APC Na Shirin Karɓar Gwamnonin Jihohi Biyu da Ke Kan Mulki

0 240

Fagen siyasar Najeriya na fuskantar sabbin sauye-sauye, yayin da akalla gwamnonin jihohi biyu da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyun adawa ke shirin komawa jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) gabanin zaɓen gama-gari na 2027.

Ana sa ran Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano da Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Plateau za su shiga APC a hukumance a wannan mako, a lokuta daban-daban.

A Kano, komawar Gwamna Yusuf zuwa APC na zuwa ne bayan ya fice daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), matakin da ya haifar da kwararar sauya sheƙa a faɗin jihar.

Ta tuna cewa manyan ’yan siyasa da dama, ciki har da ’yan Majalissar Dokokin Jihar Kano, ’yan majalissar tarayya 8, da kuma shugabannin ƙananan hukumomi 44, sun riga sun fice daga NNPP.

Mai taimaka wa Gwamna Yusuf a fannin yaɗa labarai, Bature Tofa, ya bayyana cewa shawarar gwamnan ta samo asali ne daga tarihin siyasarsa da kuma nazarinsa cewa APC ta fi zama jam’iyya mai ƙarfi da tabbatacciyar hanya wajen gudanar da mulki.

A Jihar Plateau kuwa, ana ci gaba da shirye-shirye sosai domin babban taron siyasa da ake sa ran za a gudanar a birnin Jos, inda za a tarbi Gwamna Caleb Mutfwang a hukumance cikin APC a ranar Talata.

Ana sa ran taron zai samu halartar manyan ’yan siyasa da dama, ciki har da Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, Shugaban Majalissar Dattawa, Godswill Akpabio, tare da wasu gwamnonin jihohi, ministoci da manyan jiga-jigan jam’iyya.

Da yake bayyana taron a matsayin abin tarihi, Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da wayar da Kai, Sir Joseph Ari, ya ce a cikin wata sanarwa cewa birnin Jos, babban birnin Jihar Plateau, zai zama cibiyar siyasar ƙasa a ranar taron.

Ya ƙara da cewa an kammala dukkan shirye-shiryen tarba ta musamman domin girmama gwamnan.

Leave a Reply