Yan Bindiga Sun Kashe Sifeton ‘Yan Sanda A Harin Da Suka Kai Wa Tawagar Yan Sanda A Jihar Oyo

0 132

Yan bindiga sun kai hari kan tawagar sintirin ‘yan sanda a Jihar Oyo, inda suka kasha sifeton ‘yan sanda yayin musayar wuta.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da harin, tana mai cewa wasu daga cikin maharan sun jikkata sakamakon harbin bindiga.

 Harin ya faru ne da misalin karfe 1:30 na rana a ranar Asabar, a mashigar iyaka ta Budo Masalasi da ke Jihar Oyo.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Ayanlade Olayinka, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ga manema labarai a Ibadan, babban birnin jihar.

Akalla ‘yan bindiga 10 zuwa 15 ne suka kai harin kan tawagar da mataimakin sufeton ‘yan sanda Entonu Shaibu ke jagoranta, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar sifeto Aliu Oluwole.

Maharan sun kuma yi gaba da  bindigar AK-47 ta marigayin tare da harsasai 30, yayin da kwamishinan ‘yan sanda Femi Haruna ya bayar da umarnin farautar masu laifin.

 Rundunar ‘yan sanda ta bukaci al’umma su kwantar da hankali, su kasance masu sa ido, tare da kai rahoton duk wanda ke da raunin harbin bindiga ko yake neman magani.

Leave a Reply