Gwamnati Mai Ci Ta Fi Ta Baya Tabarbarewa Ta Cancanci A Tsige Ta El-Rufai

0 191

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce gwamnatin tarayya ta yanzu ta yi aiki ƙasa da yadda shi da sauran mutane suka zata, musamman a ɓangarorin tsaro da shugabanci.
Da yake magana a shirin ARISE TV Prime Time, El-Rufai ya ce halin da ƙasar ke ciki ya tabarbare fiye da yadda ya zata a lokacin yaƙin neman zaɓe.
“Da ka tambaye ni a 2022 ko 2023 lokacin da muke yaƙin neman zaɓe cewa abubuwa za su taɓa yin muni haka, da zan ce kana da matsalar hankali,” in ji shi.
El-Rufai ya yi tambaya kan yadda ake tafiyar da kuɗaɗen gwamnati, inda ya yi zargin cewa kusan dala biliyan 100 ake cirewa kowane wata daga Asusun Tarayya (Federation Account) ba tare da amincewar Majalissar Tarayya da majalissun dokokin jihohi ba.
“Bayanan gwamnati ne, ba wai maganar da na ƙirƙira ba. Wannan dala biliyan 100 da ke fita kowane wata daga Asusun Tarayya, ba tare da amincewar Majalissar Tarayya ba, haka kuma ba tare da amincewar majalissun jihohi ba, alhali wani ɓangare na kuɗin na jihohi ne, kuma ya kamata kowace majalissar jiha ta amince da nata kaso,” in ji shi.
A cewarsa, irin waɗannan cire-cire da kashe kuɗaɗe ba sa bisa doka kuma sun kai matsayin laifin da ya cancanci tsige shugaban ƙasa.
“Saboda haka duk wannan cirewa da kashe kuɗaɗen ba sa bisa tsarin mulki. Laifi ne da ya cancanci tsige shugaba,” in ji El-Rufai.
Ya ƙara da cewa ana zargin wannan al’amari ya shafe sama da watanni 15 yana gudana, lamarin da ya tayar da hankula kan gaskiya da riƙon amana.
“Don haka ina wannan dala tiriliyan 1.5 ta tafi? Me ake amfani da ita?” ya tambaya.
El-Rufai ya kuma danganta wannan kashe kuɗaɗe da tabarbarewar tsaro, yana tambaya me ya sa matsalar tsaro ke ƙara muni duk da yawan kuɗaɗen da ake kashewa.
“Me ya sa matsalar tsaro ke ƙara tabarbarewa? Me ya sa gwamnati ke cewa al’ummomi su kare kansu?” ya tambaya.
A ƙarshe, El-Rufai ya bayyana a sarari cewa, a ganinsa, gwamnatin Shugaban Ƙasa ta yi aiki ƙasa da yadda ake tsammani.

Leave a Reply