Jiragen Ƙasa Biyu Sun Yi Taho Mu Gama da Juna A Kudancin Sifaniya.

0 269

Akalla mutum 39 sun rasa ransu sannan wasu da dama sun jikkata bayan wasu jiragen ƙasa biyu sun yi taho mu gama da juna a kudancin Sifaniya.

Ɗaya daga cikin jiragen na kan hanyarsa ne daga Malaga zuwa Madrid inda ya kauce wa hanyarsa, ya koma kan ɗaya layin dogon da a nan ne suka yi karo da wani jirgin da ke tafiya a kan layin dogon.

Firaiministan Sifaniya, Pedro Sanchez ya bayyana lamarin a matsayin abin tashin hankali da kaɗuwa.

Leave a Reply