Jirgin jigilar dalibai da yan Najeriya mazauna kasar Ukraine na cigaba da kwaso masu ra’ayin dawowa gida

0 64

Jirgin Jigilar Dalibai da yan Najeriya mazauna kasar Ukraine na biyu ya dira a birnin tarayya Abuja da yammacin jiya Juma’a, 4 ga watan Maris, 2022.

Channels TV ya rawaito cewa Jirgin Air Peace dauke da yan Najeriyan ya dira tashar Nnamdi Azikiwe misalin karfe 6:35 na yammacin jiya.

Wannan shine kashi na biyu na yan Najeriya da aka kwaso daga Ukraine.

Jirgi na biyu ya kwaso yan Najeriya da aka kwaso a yayin da ake tsaka da yakin Rasha da Ukraine, inda ya sauke su a babban birnin tarayya, Abuja.

Jirgin Max Air ya isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 7:11 na safiyar jiya Juma’a.

Manema Labarai sun rawaito cewa gwamnatin tarayya za ta baiwa kowannen su dala 100.

Manema sun ruwaito cewa wani babban jami’in gwamnati na cewa wasu cikin wadanda ake kokarin jigila sun ki hawa jirgi saboda basu son dawowa Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: