Jirgin sama ya goce daga kan titin sa a filin jirgin saman Ibadan

0 181

Wani jirgin sama mai zaman kansa dauke da shahararrun mutane 10 (VIPs) ya goce daga kan titin sa filin jirgin saman Ibadan a babban birnin jihar Oyo.

Wata majiya mai tushe ta ce lamarin ya faru ne a jiya da misalin karfe 11 na safe a filin jirgin sama na Samuel Ladoke Akintola.

Jirgin mai saukar ungulu ya fada cikin daji da ke kusa maimakon titin sa.

Nan take aka baza jami’an bayar da daukin gaggawa dana kashe gobara na filayen jiragen sama  na kasa. Sai dai ba a sami rahoton mutuwa ko jikkata ba.

Da aka tuntubi mai magana da yawun Hukumar Binciken Tsaro ta kasa (NSIB) Tunji Oketunmbi, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce an tura wata tawaga zuwa wurin domin gudanar da bincike.

Yawan hatsari a fannun sufurin jiragen sama a cikin ‘yan watannin da suka gabata ya karu a kasa, duk da korar da kuma maye gurbin shugabannin hukumomin sufurin jiragen sama. A watan Nuwamba, Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya tsallake rijiya da baya a lokacin da wani jirgin da yake ciki ya yi hatsari a filin jirgin saman na Samuel Ladoke Akintola.

Leave a Reply

%d bloggers like this: