An umarci sassan gwamnati da aiwatar da tsauraran manufofin inshorar rayuwa

0 197

Shugabar ma’aikata ta tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan, ta uamarci jami’an shugabannin ma’aikatu, da hukumomi da sassan gwamnatin kan aiwatar da tsauraran manufofin inshorar rayuwa da kuma biyan hakkokin iyalan ma’aikatan gwamnatin tarayya da suka mutu a bakin aiki.

Ta yi wannan kiran ne a jiya Juma’a a Abuja a yayin wani taro da sashen kula da inshorar inshora ya shirya.

Daraktan yada labarai na ofishinta, Mallam Mohammed Ahmed, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa Yemi-Esan wacce ta samu wakilcin babban sakataren ofishin ta Dakta Kemi Adeosun a wajen taron.

Ta kuma yi kira ga jami’an da su rungumi al’adar ci gaba da ingantawa don gaggauta biyan kodaden inshorar ma’aikatan gwamnati. Ta kuma nanata cewa hanzarta aiwatar da bayanan da suka dace na ma’aikatan da suka mutu zai taimaka wajen samar da isassun tanadin kasafin kudi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: