Kamfanin FCMB ya bayar da rahotan karuwar damfara da ayyukan bogi da kashi 637.99

0 136

Kamfanin FCMB, mamallakin bankin FCMB ya bayar da rahotan karuwar damfara da ayyukan bogi da kashi 637.99 daga naira miliyan 123 a 2022 zuwa naira miliyan 908.3 zuwa karshen shekarar 2023 data gabata.

Bankin ya bayyana haka ne a rahotan jin bahasin na shekara-shekara a desembar 2023 wanda aka fitar ranar juma’a 26 ga watan junairun nan.

Binciken ya bayyana alkaluman damfarar da boge na bana sune mafi yawa da bankin ya taba fuskanta cikin shekaru 5 da suka gabata na baya-bayan nan. Haka kuma alkaluman na nuni da kashi 65.23 na jumillar naira biliyan 1.39 da bankin ya kashe a fannin damfara da boge tun daga 2019.

Leave a Reply

%d bloggers like this: