Ma’aikatan CBN 1,500 ne zasu koma sabon ofishin su dake Ikko a jihar Legas

0 136

Akalla ma’aikata dubu 1 da 500 na babban bankin kasa CBN ne a ranar juma’a zasu koma bakin aiki a sabon ofishin su dake Ikko bayan sauya hedkwatar babban bankin zuwa Legas.

Wata majiya daga babban bankin ta bayyana duk da korafe-korafen jama’a har yanzu bankin bai sauya shirinsa na sauya matsugunin sashin bankin ba, majiyar tace duk da haka wadanda sunayen su ya fito zasu koma aiki a ranar juma’a mai zuwa.

Sabon cigaban na zuwa ne bayan matakin shugabancin bankin na sauya wasu sassan sa zuwa Legas saboda tsaron ma’aikata, da bunkasar harkokin bankin tare da rage cinkoso a hedikwatar babban bankin.

CBN yace matakin ya zama wajibi ne lura da dalilai da dama ciki har da bukatar hadin guiwa domin samar da kyakkyawan yanayi ga ma’aikata. Bankin ya kara da cewa matakin yayi dai-dai da dokokin da suka kafa bankin, sboda bayanan dake gargadi kan cinkoson ma’aikata a babban ofishin bankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: