Najeriya ta bayyana damuwa kan kalaman gwamnatin sojin Jamahuriyar nijar na ayyana ficewa kasashen Mali da Burkina Faso daga kungiya raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS.
Cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin waje ta fitar, ta bayyana irin hidimar da kungiyar ta ECOWAS tayi na tsawon rabin karni wajen tabbatar da zaman lafiya, hadinkai da cigaban deokradiyya a yankin Sahel.
Tayi bayanin cewa Najeriya tana goyon bayan matakin ECOWAS na cigaba da karfafa yunkurin yanci da walwalar dukkan yan kasashe membobin ta.
Sanarwar ta kuma kara da cewa Najeriya tayi aiki bisa kyakkyawan yakinin ganin an shawo kan matsaloli da kalubalen cikin gida. Kazalika ta kara da cewa, kofofin Najeriya a bude suke domin tattaunawa da kasashen Burkina Faso, Nijer da Mali, ta yadda dukkan al’ummar yankin zasu cigaba da cin moriyar bunkasar tattalin arziki da cigaban demokradiyyar da kungiyar tayi amanna da ita.