Kamfanonin Jiragen Saman Kasarnan Sun Amince Su Yi Jigilar Maniyyatan Najeriya Zuwa Aikin Hajji

0 93

Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON da kamfanonin jiragen sama guda hudu da za su yi jigilar maniyyatan Najeriya zuwa aikin hajjin bana sun cimma matsaya.

Kamfanonin jiragen saman sun hada da Aero Contractors, da Air Peace, da Azman Air da kuma Max Air.

Wakilan kamfanonin jiragen saman a makon da ya gabata sun ki sanya hannu kan yarjejeniyar saboda rikicin Sudan da ya jawo yin zagaye, lamarin da ya sanya suke fargabar zai iya haifar da karin kudin Hajji.

Amma a zaman yarjejeniyar da aka sake a Abuja, kamfanonin jiragen saman sun sanya hannu kan yarjejeniyar ba tare da karin kudin Hajji ba.

A cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai na hukumar Mousa Ubandawaki ya fitar, shugaban hukumar Zikrullah Hassan ya yabawa kishin kasa da kamfanonin jiragen sama suka nuna duk da kalubalen da rikicin kasar Sudan ya haifar. Manajan Daraktan kamfanin Aero Contractors, Ado Sanusi, ya ce kamfanonin jiragen saman na sane da halin da alhazan da suka biya kudin aikin hajji kafin rikicin ya barke ke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: