Kimanin manoman shinkafa dubu 40 ne zasu samu tallafin noma na Anchor Borrowers a jihar Kano domin sake bunkasa shinkafa a Najeriya

0 84

Kimanin Manoman Shinkafa dubu 40, ne zasu samu tallafin Noma Dan Riba na Gwamnatin tarayya wato Anchor Borrowers a Jihar Kano domin sake bunkasa Shinkafa a Kasar nan.

Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa reshen Jihar Kano Alhaji Abubakar Aliyu, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN a Kano.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ya rawaito cewa Anchor Borrowers Programme, wani shiri ne da gwamnatin tarayya ta kirkira domin karfafa gwiwar Manoma ta hanyar samun horo, da basu kudade da kuma nuna musu kasuwar da zasu sayar da kayan su da Daraja.

Haka kuma shirin Anchor Borrowers Programme hadin gwiwa ne tsakanin Babban Bankin Kasa wato CBN da sauran bankuna da kuma gwamnatocin Jihohi domin bunkasa tattalin arzikin kasa.

Alhaji Abubakar Aliyu, ya ce shirin zai samar da takin zamani da irin Shinkafa dubu 15,000 a lokacin noman rani, inda kuma zasu sake samar da karin dubu 25,000 ga wasu Manoman domin yin Noma a lokacin Damina.

Leave a Reply

%d bloggers like this: