Ma’aikatar Aikin Gona Da Raya Karkara ta Kasa ta fara gudanar da rigakafin cututtukan dabbobi a jihar Jigawa

0 72

Ma’aikatar Aikin Gona Da Raya Karkara ta Kasa ta fara gudanar da rigakafin cututtukan Dabbobi a yankin Arewa maso yammacin kasar nan.

An fara gudanar da rigakafin ne a karamar hukumar Maigatari biyo bayan yadda garin yake kan Iyaka, kamar yadda hakan yake cikin kudurin gwamnatin tarayya na dakile cututtuka masu kwarara a sassan kasar nan.

Da yake kaddamar da rigakafin Ministan Aikin Gona Dr Muhammad Mahmoud Abubakar, ya ce za’a gudanar da rigakafin ne a kowacce Shiya ta kasar nan guda 6.

Ministan wanda Daraktar Lafiyar Dabbobi Dr Maimuna Abdullahi Habib, ta wakilta ya bayyana cewa kiwon Dabbobi na daya daga cikin hanyoyin da suke samar da kaso 70 na ayyukan yi a kasar nan.

Haka kuma ta ce kiwon na samar da bunkasar tattalin arzikin kasa, da wadatar Abinci da kuma hanyoyin dogaro da kai musamman ga mazauna karkara.

Ministan ya ce a yanzu hakan akwai kimanin Shanu Miliyan 22 da dubu 300, da Tumakai Miliyan 53 da 600 da Awakai Miliyan 99 da dubu 800 da Aladai Miliyan 9 da dubu 200 da kuma Kaji Miliyan 425 da dubu 700 a shiyoyi 6 na kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: