Rundunar yan sandan jihar Zamfara sun kubutar da mutane 39 wanda akasarin su mata da kananan yara da aka yi garkuwa da su a jihar

0 61

Rundunar yan sandan Jihar Zamfara, sun kubutar da mutane 39 wanda akasarin su Mata da Kananan Yara da aka yi garkuwa da su a Jihar.

An sace mutanen ne a watan Maris da Afrilun cikin wannan shekara a kyauyikan Kananan Hukumomin Bungudu da Maru na Jihar.

Kwamishinan Yan sandan Jihar Ayuba Elkanah, shine ya tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a yau.

A cewarsa, Jami’an su da suke sunturi tare da Sojoji sunyi nasarar shiga Majalisar Dabar Magaji wanda take Dajin Kadanya, a mahadar kananan hukumomin Kaura Namoda da Maradun na Jihar inda suka kubutar da mutanen.

Haka kuma ya ce rundunar ta kama mutane 10 ciki harda Yan Sa kai bisa zargin su da aikata laifuka daban-daban.

Cikin kayayyakin da rundunar ta karbo sun hada da Bindigogi kirar hannu, da Babura, da kuma sauran kayan laifi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: