Ma’aikatar Jinkai, Iftila’I da Cigaban Al’umma ta ce zata kashe Naira biliyan 6 da miliyan 200 domin horas da matasa sama da dubu 16 sana’oin dogaro da kai a jihar Bauchi

0 70

Gwamnatin tarayya, karkashin Ma’aikatar Jinkai, Iftila’I da Cigaban Al’umma ta ce zata kashe Naira Biliyan 6 da Miliyan 200 domin horas da Matasa dubu 16 da 820 Sana’oin Dogaro da kansu musamman a fannin gyaran Wayar hannu da sauran su.

Ministar Ma’aikatar Hajiya Sadiya Umar Farouk, ita ce ta bayyana hakan a lokacin da take kaddamar bada horo kan gyaran wayoyi a Bauchi, inda ta ce horon ya kunshi masu Karatu da Marasa Karatu ta fannin N-Skills.

Haka kuma ta ce hakan yana cikin kudurin gwamnatin shugaban Kasa Muhammadu Buhari na fitar da yan Najeriya Miliyan 100 daga cikin Talauci cikin shekaru 10 masu zuwa.

Hajiya Sadiya Umar Farouk, ta ce idan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince a sake fadada shirin yaki da Talauci, Ma’aikatar ta zata sake kirkirar hanyoyin samar da Sana’oi ga Matasan Jihar ta Bauchi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: