Kimanin Mutane 222,600,000 Ne Ke Amfani Da Wayoyin Hannu A Najeriya

0 73

Hakumar kididdiga ta kasa NBS tace kimanin mutane miliyan 222, da dubu 600 ne ke amfani da wayoyin hannu a Najeriya, a wani rahoton karshen shekarar 2022 da ta fitar.
Alkaluman masu ta’ammali da wayoyin hannun ya karu da kaso 27.1, idan akayi la’akari da yawan wasu amfani da wayar a shekarar 2021 su miliyan 195 da dubu 500.
Wannan da na kunshe cikin rahotan da hakumar ta fitar yau a birnin tarayya Abuja.
NBS tace yawan masu amfani da yanar gizo ya zuwa karshen shekarar data gabata ya kai miliyan 154 da dubu 900, idan akayi la’akari da yawan masu amfani da yanar zigon a 2021 su miliyan 142.
Rahotan ya nuna cewa jihar Legas ce kan gaba a yawan masu amfani da wayar ta hannu, inda mutane miliyan 26 da dubu 500 ke ta’ammali da ita, sai jihar Ogun mai mutane miliyan 13.
Jihar kano ce a mataki na 3 na yawan masu amfani da wayar hannu a Najeriya inda yawan su ya kai miliyan 12 da dubu 400.

Leave a Reply

%d bloggers like this: