Shugaba Buhari Zai Bar Abuja A Yau Zuwa Birnin Accra Na Kasar Ghana

0 105

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja a yau zuwa birnin Accra a kasar Ghana domin halartar taro na musamman da shugabannin kasashen hukumar gabar kogin Guinea karo na 3.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya sanar jiya a Abuja cewa shugaban kasar Ghana Nana Akuffo Ado ne ya kira taron.

A cewar Femi Adesina, an tsara cewa shugaban kasar zai halarci taron, tare dayin jawabi a tattaunawar da za ayi akan hanyoyin karfafa zaman lafiya da tsaro a yakin da ake yi da laifukan da ake aikawata a ruwa da gabar kogin.

Shugaba Buhari zai samu rakiyar ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, da babban mai bawa shugaban kasa shawara akan tsaro, Babagana Monguno, da kuma darakta janar na hukumar liken asiri ta kasa, Ahmed Abubakar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: