Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Kaddamar Da Shirin Noman Rani Na Gari A Gobe

0 84

Gwamnatin tarayya ta shirya kaddamar da shirin noman rani na Gari wanda yake a jihohin Jigawa da Kano a gobe.

Hakan na bisa turbar jajircewar shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen fadada hanyoyin tattalin arziki da tabbatar da wadatar abinci da bunkasa jin dadin ‘yan Najeriya.

Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da aka fitar a jiya daga hukumar ma’aikatar albarkatun ruwa, dauke da sa hannun babbar sakatariyar ma’aikatar, Didi Esther Wal­son-Jack.

Kamar yadda yazo a sanarwar, Ministan Albarkatun Ruwa, Engineer Suleiman Adamu, zai kaddamar da aikin a wajen da aka assasa shirin noman ranin na Gari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: