Kamfanonin Jiragen Saman Najeriya Na Neman Karin Kujerun Maniyyata Hajjin Bana

0 73

Gabannin aikin jigilar alhazai zuwa Saudiyya da za a fara a ranar 21 ga watan Mayu, kamfanonin jiragen saman Najeriya na neman karin kujerun maniyyata, inda suka soki tsarin da ake kai a yanzu.

Kamfanonin jiragen saman sun yi ikirarin cewa tsarin da ake kai a yanzu da ya kunshi kasashe da dama, ciki har da Najriya, inda kamfanonin jiragen saman Saudi aka ware musu kaso 50 cikin 100 na alhazan, ba zai taimakawa cigaban kamfanonin jiragen saman sauran kasashen ba.

Amma wasu masana sun ce duk da shakkar da ake da ita kan kamfanonin jiragen saman Najeriya kamar yadda wasu daga cikinsu suka kasa aikin da aka basu a shekarun baya, duk da hakan ba laifin bane su nemi karin kujeru.

An bayar da labarin cewa wani kamfanin jiragen sama na Saudiyya, FlyNas, shi ake sa ran zai kwashe kashi 40 cikin 100 na maniyyatan Najeriya, yayin da sauran kamfanonin Najeriya guda 6 da suka shiga aikin, za su kwashe kashi 60 cikin 100.

Hakan na bisa turbar tsarin rabo daga gwamnatin Saudiyya, wanda ya bawa kamfanonin jiragen Saudi damar kwashi kashi 50 cikin 100 na maniyyatan kowace kasa da za su je aikin Hajji.

Leave a Reply

%d bloggers like this: