Kimanin mutum 12 ne suka mutu yayin da wasu 12 kuma suka samu raunika biyo bayan wani hadarin mota da ya afku a hanyar Patiskum zuwa Bauchi

0 139

Kimanin Mutane 12 ne suka mutu, yayin da wasu 12 kuma suka samu raunika biyo bayan wani hadarin Mota da ya afku a hanyar Patiskum zuwa Bauchi da ke Jihar Yobe.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Afkuwar Hadura na shiyoyin Borno, Yobe, da kuma Bauchi Mista Rotimi Adeleye, shine ya tabbatar da hakan ga manema Labarai.

A cewarsa, lamarin ya faru ne kusa da kyauyen Lanzai wanda yake da nisan Kilomita 45 tsakanin sa da Patiskum na Jihar.

Kwamandan ya dora alhakin faruwar hadarin kan gudun wuce sana’a da kum tukin ganganci.

Haka kuma, ya bukaci masu sarautun gargajiya da shugabanNIN Addinai su tallafawa hukumar wajen fadakar da Al’umma kan Illar tukin ganganci da kuma gudun wuce sa’a.

Kazalika, ya ce gawarwakin mutanen da suka mutu a hadarin suna Asibitin Patiskum a sashen Ajiyar gawarwaki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: