Ministan harkokin wajen China ya bayyana goyon bayan kasarsa ga Rasha kan mamayar da ta ke yi a Ukraine

0 49

Ministan harkokin wajen China, Wang Yi ya bayyana goyon bayan kasarsa ga Rasha kan mamayar da ta ke yi a Ukraine.

Manema Labarai sun rawaito cewa an ga wani rahoton, wanda a ciki ministan ke cewa duk yadda yanayin siyasar duniya zai rikice, China da Rasha za su ci gaba da renon dangantakarsu mai matukar muhimmanci.

Mista Wang ya bayyana China da Rasha a matsayin mawabta kuma makusantan kasashe masu muradu iri daya.

Haka kuma ya ce dangantaka ce ta kut-da-kut wadda kusan babu irinta a duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: