Rahotanni na cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a Najeriya ta umurci gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya sauka daga daga mukaminsa.

Kazalika kotun ta umurci mataimakin gwamnan da kakakin majalisar dokokin jihar da sauran ƴan majalisar da suka sauya sheka tare da gwamnan daga jam’iyyar PDP zuwa APC su ma su Sauka daga mukamansu.

Kotun ta ce sauya shekar da suka yi daga jam`iyyar PDP zuwa APC ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya, saboda haka ba su cancanci zama a kan kujerun nasu ba.

Harwayau, kotun buƙaci su da su mayar da bako dayan albashin da suka karba bayan sauya shekar tasu.

BBCHausa

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: