

- Mataimakin Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi, shine ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jam’iyyar APC - May 27, 2022
- Shugaba Buhari yace gwamnatinsa tana assasa ginshiki mai inganci na kyakykyawar rayuwa domin yara manyan gobe a Najeriya - May 27, 2022
- Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta haramta bangar siyasa da tare da yin amfani da duk wani makami ga yaran yan siyasa - May 27, 2022
Gwamnatin Jihar Jigawa ta nanata kudurin ta na cigaban da fadada hanyoyin bunkasar tattalin arzikin Jihar, ta fuskar fadada kudaden Rabanu da kuma rage kashe-kashen kudade.
Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake duba sabon Kamfanin da aka bude a Jihar nan.
A cewarsa, rawar da bangarang Masana’antu yake takawa abune mai matukar muhimmanci, wajen samar da ayyukan yi ga mutanen da suke wurin da aka yi Kamfanin.
Gwamna Badaru Abubakar, ya ce gwamnatin sa, ta hannun hukumar lura da cigaban masu zuba Jari, zasu tallafawa masu masana’antu a jihar nan.
Haka kuma ya ce kimanin Kadada 500 gwamnatin Jiha ta bawa Kamfanin domin kafa cibiyar da zata bawa Manoman Rini Horo, ta yadda Manoman Jihar dama kasashen yammacin Afrika zasu amfana.
Kazalika, ya godewa Kamfanin bisa kaddamar da Gona da kuma Cibiyar da zata bawa Manoman Rini horo kan yadda zasu Noma Ridi a lokacin Rani da kuma gyara shi.