Majalisar wakilai ta canja matsayarta akan gyaran wasu dokoki uku da suka shafi mata

0 77

Majalisar wakilai ta canja matsayarta akan gyaran wasu dokoki uku da suka shafi mata.

Dan majalisa, Hon Abubakar Hassan Fulata, na jam’iyyar APC daga jihar Jigawa ne ya mika kudirin canja matsayar akan dokokin guda uku da suka hada da karin iko ga mata wajen gudanar da jam’iyyun siyasa da abubuwan da ake bukata domin kasancewa dan asalin gari ko jiha.

Sai dai, Hassan Fulata bai hada da kudirin warewa mata kashi 20 cikin 100 na mukaman siyasa a tarayya da jihoshi ba.

Watsi da kudirorin ya jawo zanga-zanga a kofar shiga majalisun kasarnan, inda kungiyoyin mata ke kiran majalisun sun canja matsayarsu.

Da yake gabatar da kudirin canja matsayar, Hassan Fulata yace akwai bukatar majalisar ta dakatar da dokokinta domin canja matsayarta akan kudirorin.

Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, yayi nuni da cewa yunkurin majalisar ya sabawa al’adar gyaran kudin tsarin mulki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: