

- Anyi hasashen samun ruwan sama hade da tsawa a fadin kasarnan daga yau zuwa ranar Laraba - August 23, 2021
- Wata kungiyar adawa ta ce tana da dubban mayaka da zasu fafata yaki da yan Taliban a Afghanistan - August 23, 2021
- ‘Yan bindiga sun kashe mutane 4 tare da sace wasu 50 a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara - August 23, 2021
Wata Babbar Kotun Tarayya dake zamanta a Kano ta umarci Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano da ta dakatar da binciken da take yi wa Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II bisa zargin kashe biliyoyin kuɗi ba daidai ba.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar 7 ga watan Yuni ne Muhammad Munnir Sanusi, mai riƙe da muƙamin Ɗamburan Kano, kuma Shugaban Ma’aikatan Sarki Sanusi ya garzaya kotu, inda yake roƙon ta da ta dakatar da Gwamnatin Jiha ko wakilanta daga ɗaukar mataki na gaba game da rahoton farko da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kanon ta fitar.
A hukuncin da ya yanke ranar Talata, Mai Shari’a O A. Egwuatu ya dakatar da Hukumar Yaƙi da Cin Hancin game da ɗaukar kowane irin mataki a kan Sarki Sanusi har sai ta kammala jin ƙarar da aka shigar gabanta ranar 7 ga watan YuniDaga sai Mai Shari’a Egwuatu ya ɗage yanke hukuncin har sai ranar 28 ga watan Yuni.