Kotu ta yanke wa mutum huɗu hukuncin ɗaurin rai da rai a jihar Jigawa

0 374

Wata Babbar Kotu ta yanke wa mutum huɗu hukuncin ɗaurin rai da rai bayan samunsu da laifin yi wa ’yar shekara 14 fyaɗe a unguwar Kurmi da ke Ƙaramar Hukumar Gwaram a Jihar Jigawa.

Waɗanda aka yanke wa hukuncin sun haɗa da Sale Ibrahim mai shekara 40, Amadu Saleh mai shekara 46, Sale Ali mai shekara 40, da Danlami Yusuf mai shekara 37.

Lauyan masu ƙara ya gabatar da shaidu huɗu da suka haɗa da rahoton likita tare da gabatar da shaidu guda biyu don tabbatar da tuhumar da yake yi wa ababen zargin.

Bayan sauraron dukkan ɓangarorin biyu a shari’ar, kotun ta ce lauyan masu ƙara ya gamsar da kotun da hujjojin da ya gabatar wanda babu shakka a kansu.

Dangane da hakan ne kotun ta samu waɗanda ake tuhuma da laifin fyaɗe wanda ya saba wa sashe na 3 (1) da kuma hukuncin da ya dace a ƙarƙashin sashe na 3 na dokokin Jihar Jigawa Idan ba a manta ba, a kwanakin baya ne babbar kotun jihar ta yanke wa wani mutum, Aminu Ali mai shekara 25 hukuncin ɗaurin rai da rai bisa samunsa da laifin aikata fyaɗe da luwaɗi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: