Kotu ta yanke wa wasu ‘yan kasuwa hukuncin daurin watanni bakwai a gidan yari

0 304

Wata kotu a Jos dake jihar Filato ta yanke wa wasu ‘yan kasuwa uku, Usman Ibrahim mai shekaru 29, da Ibrahim Kabiru shekaru 36 da Mohammed Abubakar shekaru 30 hukuncin daurin watanni bakwai a gidan yari, kowannensu bisa zargin wani mutum da laifin maita inda suka masa duka.

Alkalin kotun, Shawomi Bokkos, ta yanke wa wadanda ake tuhumar hukuncin ne a jiya Alhamis bayan sun amsa laifin da ake tuhumarsu.

Sai dai kotun ta ba su zabin tarar Naira dubu 50,000, sannan kuma ya umarce su da su biya N100,000 kowannen su a matsayin diyya ga wanda ya shigar da karar.

Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, sifeto Monday Dabit, ya shaida wa kotun cewa an kai karar ne a ranar 6 ga watan Satumba, ta hannun wani mutum mai suna Zakari Sabo. Lauyan mai gabatar da kara ya ce wadanda ake tuhumar sun kai wa wanda ake karar hari ne inda suka zarge shi da maita, suka yi masa duka, tare da yayyaga masa tufafi da kuma karya hannunsa na dama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: