Rikicin Fulani da ’yan banga yayi sanadiyyar mutuwar mutum biyu a Jihar Neja

0 180

An tabbatar da mutuwar mutane biyu, yayin da wasu bakwai ke ci gaba da karbar magani a cibiyar kiwon lafiya matakin farko da ke Beji, bayan wani rikici da ya barke tsakanin Fulani da ’yan banga a kasuwar mako-mako ta Beji da ke karamar hukumar Bosso ta Jihar Neja.

Mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yammacin ranar Laraba lokacin da ake tsaka da hada hada a Kasuwar.

Mataimakin Shugaban Cibiyar Kiwon Lafiya a matakin farko ta Beji, Aliyu Yusuf, ya tabbatar wa da jaridar Daily Trust cewa ya ziyarci asibitin a ranar Alhamis da ta gabata cewa an kawo wadanda suka jikkata guda tara zuwa asibitin da raunuka daban-daban. Ya ce an tabbatar da mutuwar mutane biyu, yayin da sauran mutane bakwai wadanda dukkansu Fulani ne, ke cigaba da karbar magani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: