An kama wani da ake zargin dan fashi da makami ne a jihar Bauchi

0 173

An kama wani da ake zargin dan fashi da makami ne a dakin taro na makarantar Bishop Moore Memorial School da ke jihar Bauchi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Wakil ya ce jami’an da ke aiki a sashin GRA karkashin jagorancin DPO tare da ‘yan banga sun dakile wani yunkurin kai harin fashi da makami da aka yi a makarantar tunawa da Bishop Moore a ranar 4 ga Nuwamba, 2023, da misalin karfe 4:30. Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun bi diddiginsu zuwa wata maboyarsu da ke kusa da wani tsauni, amma sai aka bi su aka kama su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: